Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Kenya ya bayyana a ranar Litinin cewa, yana shirin kara megawatt 511 na makamashi mai tsafta wajen samar da wutar lantarki nan da karshen shekarar 2018.
Darektan KenGen, wato kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Kenya, Albert Mugo, ya bayyana a yayin wani taron masu zuba jari a birnin Nairobi cewa, gina tashoshin farko na samar da megawatt 70 na makamashi mai tsafta zai fara a farkon watanni uku na shekarar 2016.
Tuni mun samu alkawarin kudi daga hukumomin kasa da kasa da gwamnati na dalar Amurka miliyan 314 da ake bukata wajen gina tashar wutar lantarki ta magawatt 70, in ji mista Mugo.
Mista Mugo ya bayyana cewa, kamfaninsa na shirin kashe dalar Amurka biliyan 1,75 domin samar da magawatt 431 daga makamashi mai tsafta da kuma magawatt 80 daga karfin iska.
Yanzu muna mai da hankali kan makamashi mai tsafta domin rage dogaro daga makamashin karfin ruwa da matsalar samun ruwan sama, in ji mista Mugo.
Shekarar bara, kamfanin KenGen ya kara karfinsa na samar da wutar lantarki zuwa megawatt 1611. (Maman Ada)