in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon na karfafa karfin MDD wajen samar da makamashi mai tsafta
2015-09-17 10:28:03 cri

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya sanar a ranar Laraba da kafa wata sabuwar hukuma dake da manufar samar da makamashi mai tsafta ga kowa, da zummar saukaka aikin aiwatar da wani sabon shirin ci gaba na kungiyar na nan gaba.

Makamashi yana matsayin wata jar igiya dake hada bunkasuwar tattalin arziki, adalci tsakanin al'umma da kuma muhalli mai tsafta. Ina nuna yabo sosai game da shigar da muradun ci gaba mai karko na lamba bakwai kan makamashi a cikin shirin ci gaba zuwa na shekarar 2030, in ji mista Ban Ki-moon a yayin wani zaman taro tare da kasashe mambobi a cibiyar MDD, dake birnin New York.

Muradu goma sha bakwai na ci gaba mai karko (ODD) wadanda ya kamata shugabannin kasashen duniya su amince a karshen wata, an tsara su ne domin ci gaba da tafiyar da kokarin da aka fara na muradun sabon karni na ci gaba (OMD) a tsawon shekaru goma sha biyar masu zuwa. Za su zama wani sabon shirin ci gaba mai karko na MDD, kuma za su kasance da nufin kawar tsananin talauci nan da shekarar 2030. A cewarsa, shirin ODD na lamba bakwai, an kebe shi wajen samar da makamashi mai arha, da inganci, da karko kuma na zamani ga kowa.

Makasudin taron ranar Laraba shi ne sanar da kasashe mambobi kan ci gaban da aka samu na baya bayan nan kan shirin "makamashi mai tsafta ga kowa" da sakatare janar na MDD ya kaddamar yau da kusan shekaru hudu, wanda kuma bisa shi ne yake son yin dogaro domin aiwatar da shirin ODD na bakwai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China