in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da iko kan tekun kudancin kasar
2016-07-05 11:22:17 cri
Babban lauyan kasar Philippines dake kula da hukuncin tekun kudancin kasar Sin Paul Reichler ya bayyana cewa, bisa hukuncin da za a yanke kan batun, za a yi watsi da ikon kasar Sin kan tekun kudancin kasar, dangane da wannan lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi a jiya Litinin cewa, wannan hukuncin da za a yanke shi ba ya bisa doka, kasar Sin ba za ta amince da hukuncin ba, kuma za ta ci gaba da aiwatar da ikonta kan yankin tekun kudancin kasar.

Ya kuma kara da cewa, wannan hukuncin da za a yanke bisa rokon kasar Philippines kadai ba ya da amfani, kuma ba ya bisa doron doka, ikon kasar Sin kan yankin tekun kudancin kasar yana da dogon tarihi, kasar tana kuma kiyaye ikonta bisa harkokin tarihi da dokoki yadda ya kamta, shi ya sa ba za ta amince da wannan hukuncin da za a yanke ba bisa doka ba.

Haka zalika, bisa labarin da aka samu, an ce, kwanan baya, wasu manyan jami'an siyasa da masana na kasashen ketare suna bayyana goyon bayansu ga kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar, sun kuma bayyana cewa, hanyar yin shawarwari ita ce hanyar da ta fi dacewa ga bangarorin da abin ya shafa wajen warware wannan sabani.

Tsohon mataimakin firanimistan kasar Thailand, kana shugaban kwamitin zaman lafiya da sulhu na Asiya Surakiart Sathirathai ya ce, bisa dokokin kasa da kasa, ko wace kasa a nan duniya tana da ikon amincewa ko kuma kin amincewa kan hukuncin da aka yanke kan ita, ya kamata gamayyar kasa da kasa su girmama matsayin kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar, tun da aka yanke hukunci bisa rokon kasar Philippines ita kadai, a maimakon samun amincewar kasar ta Sin.

Haka kuma, shugaban kungiyar nazarin manyan tsare-tsare ta kasar Cambodia Chheang Vanarith ya bayyana cewa, hukuncin da za a yanke ba shi da amfani wajen warware sabanin dake tsakanin Sin da Philippines kan batun tekun kudancin kasar Sin, kana ya kuma bata ran bangarorin da abin ya shafa, shi ya sa ya kamata bangarorin biyu su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari da zaman lafiya.

Kaza lika, tsohon sakataren dake kula da harkokin diflomasiyyar kasar Pakistan Riaz Rhokhar yana ganin cewa, hanyar yin shawarwari da kasar Sin ta fidda wajen warware batun tekun kudancin kasar za ta taimaka matuka wajen warware sabanin dake tsakanin bangarorin da abin ya shafa kai tsaye.

Ban da haka kuma, babban sakataren jam'iyyar kwaminis na kasar Afirka ta Kudu Blade Nzimande ya bayyana a jiya cewa, jam'iyyar tana goyon bayan kasar Sin kan batun tekun, tana kuma sa ran za a warware matsalar ta hanyar zaman lafiya da yin shawarwari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China