in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jita-jitan da wasu kasashe suka yada kan batun tekun kudancin Sin ba za su wakilci ra'ayoyin kasa da kasa ba
2016-06-14 20:00:37 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a gun taron manema labaru a yau Talata cewa, jita-jitan da wasu kasashe suka yada kan batun tekun kudancin kasar Sin ba za su boye hakikanin gaskiya ba, kana ba za su wakilci ra'ayoyin kasashen duniya ba.

Wasu na tambaya cewa, a kwanakin baya, gwamnatocin kasashen Saliyo da Kenya suka bayar da sanarwar nuna goyon bayansu ga kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar.

Haka kuma kimanin kasashe 60 ne suka nuna goyon baya ga matsayin Sin kan wannan batu, ko wannan sakamako ne da gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin samu?

Lu Kang ya amsa cewa, a hakika, batun tekun kudancin kasar Sin batu ne tsakanin Sin da wasu kasashen dake kewayen tekun kudancin kasar Sin.

A shekarun baya baya nan, wasu kasashe sun yi kokarin tada zaune-tsaye a yankin ba tare da yin la'akari da muradun jama'ar kasashen dake yankin ba, kana suka ingiza wasu kasashen dake yankin da su sabawa alkawari da ka'idoji da dokokin kasa da kasa da aka cimma da sunan "tabbatar da bin ka'idoji".

Bisa wannan hali, wasu kasashen da suka damu da kasar Sin kana kawayen kasar Sin sun nuna damuwa kan halin da ake ciki, bayan da suka gano gaskiyar lamari, kasashe da dama suka bayyana ra'ayoyinsu na hakika cikin adalci, don haka kasar Sin tana nuna yabo da godiya gare su. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China