in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma matsayi daya kan batun tekun kudancin kasar Sin a taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai
2016-06-25 12:41:47 cri

Jiya Jumma'a 24 ga wata, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ta fidda sanarwar Tashkent ta cikon shekaru 15 da kafa kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a birnin Tashkent na kasar Uzbekistan, kuma bisa sanarwar din, mambobin kasashen kungiyar sun cimma matsayi daya wajen nuna goyon baya ga kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar.

Mambobin sun tabbatar da cewa, ya kamata a kiyaye tsarin dokokin teku bisa yarjejeniyar dokokin teku ta MDD da dai sauran dokokin kasa da kasa da abin ya shafa, sa'an nan, kasashen da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari da zaman lafiya, bai kamata kasashe da bangarorin da abin bai shafa ba su tsoma baki cikin wannan batu ba.

Don gane haka, mambobin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai su yi kira da a bi yarjejeniyar dokokin tekun MDD da kuma sanarwa ta bangarorin da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa, yayin da ake aiwatar da harkokin dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Bugu da kari, an kuma tattauna batutuwan yiwa kwamitin sulhu na MDD kwaskwarima da yaki da ta'addanci da ma wasu batutuwan dake shafar yadda za a tinkari sabbin kalubaloli a duniya cikin sanarwar Tashkent, kuma mambobin sun yi kira da a gaggauta zartas da yarjejeniyar MDD da ta shafi yaki da ta'addanci daga dukkan fannoni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China