in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata bangaren da abin bai shafa ba ya tsoma baki kan batun tekun kudancin kasar Sin ba
2016-07-01 10:38:45 cri
Bisa gayyatar da hukumar yin mu'amala da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi musu, wasu jami'ai daga jam'iyyun kasashen Afirka sun kawo ziyara a kasar Sin, kuma sun bayyanawa 'yan jaridan kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya cewa, bai kamata bangaren da abin bai shafa ba ya tsoma baki kan batun tekun kudancin kasar Sin ba, kana ba a iya samar da shiri mai amfani ba wajen daidaita batun. Ya kamata kasashen da abin ya shafa da su daidaita batun ta hanyar yin shawarwari da juna.

Sakatariyar kotun yanke hukunci kan batun tekun kudancin kasar Sin da aka kafa bisa rokon kasar Philippines kadai ta bayyana a ranar 29 ga watan Yuni cewa, kotun za ta gabatar da hukuncin da aka yanke kan wannan batu a ranar 12 ga watan Yuli. Game da wannan, shugaban kawancen matasa na jam'iyyar tabbatar da demokuradiyya ta kasar Ghana ya bayyana cewa, bangarorin da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa sun zama tamkar wani reshen itace guda, idan aka yanke reshen, dukkansu za su fadi. Domin wannan batu yana shafar moriyar kasashen da abin ya shafa, tilas ne a daidaita shi ta hanyar yin shwarwari kai tsaye.

Babbar jami'ar jam'iyyar APC ta kasar Nijeriya ta bayyana cewa, bai kamata kasashen waje da abin bai shafa ba su tsoma baki kan batun tekun kudancin kasar Sin ba, tilas ne kasashen da abin ya shafa da su yi shawarwari da tattaunawa don warware batun. Kana ta nuna yabo ga kasar Sin kan yadda ba ta tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashen waje, a ganinta ya kamata sauran kasashen duniya su yi koyi da irin wannan manufa yayin da ake daidaita batun tekun kudancin kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China