in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsayin Sin da Rasha kan batun tekun kudancin Sin zai taimakawa kasashen duniya su kara fahimtar yanayin batun
2016-06-27 20:15:26 cri
A kwanan baya ne, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kawo ziyara a kasar Sin, inda ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka sanya hannu kan sanarwar Sin da Rasha da ke yayata dokokin duniya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei ya bayyana a yau a nan birnin Beijing cewa, matsayin da kasashen biyu suka bayyana a cikin wannan sanarwa zai taimakawa kasashen duniya su kara fahimtar ainihin yanayin da ake ciki game da batun tekun kudancin kasar Sin.

Bayan haka, a gun taron kolin Tashkent na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka kammala a ranar 24 ga wata, an ba da wata sanarwa, inda aka nuna goyon baya ga matsayin da Sin ke dauka kan wannan batu. A sa'i daya kuma, a kwanan baya, a matsayinta na wata babbar kasa a nahiyar Afirka, kana daya daga cikin kasashen BRICS, kasar Afirka ta Kudu ta bayyana ra'ayinta na nuna goyon baya ga matsayin Sin kan batun tekun kudancin kasar. Game da wannan batu, Hong Lei ya bayyana cewa, wannan ya nuna cewa, akwai kasashe da dama da suke nuna adalci, da kiyaye dokokin duniya, wannan ya bayyana muryoyin kasashen duniya. Ana fatan bangarorin da abin ya shafa za su saurari wadannan muryoyi, kada su yi yunkurin daidaita batun tekun kudancin kasar Sin ta hanyar da ba ta dace ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China