Sanarwar ta ce, da babbar murya ce Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da mahukuntan Isra'ila da suka dora niyyar gina sabbin gidajen kwana 560 a matsugunin Yahudawa a Ma'ale Adumim dake yammacin gabar kogin Jordan, da kuma wasu 240 a matsugunin Yahudawa a gabashin birnin Kudus.
Sanarwar ta ce, bangarorin hudu da batun Gabas ta Tsakiya ya shafa, wato MDD, da kungiyar EU, da Amurka, da kuma Rasha suka gabatar da wani rahoto domin yin kira ga Isra'ila da ta daina kafa matsugunan a kwanan baya, amma kuma abin takaici gwamnatin Isra'ila ta gabatar da wannan niyyarta. Game da hakan, Ban Ki-moon ya yi bakin ciki kwarai.
Ban Ki-moon ya nanata cewa, kafa matsugunan ya keta dokokin duniya. Ya kalubalanci gwamnatin Isra'ila da ta daina da kuma janye wannan niyya domin daddale yarjejeniyar karshe cikin zaman lafiya da adalci.(Fatima)