in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta kai ziyara kasar Rasha
2015-06-29 13:25:17 cri
Bisa gayyatar da ofishin shugaban kasar Rasha ya yi masa, shugaban sashin kula da yayata manufofin kasar Sin na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin mista Liu Qibao ya jagoranci tawagar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin don kai ziyara kasar Rasha, zai kuma gana da mataimakin direkta na farko a ofishin shugaban kasar Rasha Alexey Gromov a birnin St.Petersburg, tare da halartar dandalin tattaunawa kan harkokin kafofin watsa labaru na Sin da Rasha.

Liu Qibao ya yi jawabi a dandalin tattaunawar cewa,kamata ya yi kafofin watsa labaru na kasashen biyu su bi tunanin hadin gwiwa da yin imani da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu don sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni, da raya zirin tattalin arziki na hanyar Siliki, da gina kawancen tattalin arziki tsakanin Asiya da Turai, da kiyaye nasarar yakin duniya na biyu da nuna adalci tsakanin kasa da kasa, da yin mu'amala da juna a fannin al'adu, da sada zumunta da juna, da kuma watsa labarai na zahiri ga duniya gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China