Kawo yanzu, an samu muryoyin kasa da kasa cikin adalci. Mafi yawan kasashe da kungiyoyin duniya da suka bayyana rashin amincewarsu ta hanyoyi daban daban kan ba da labarai na son rai da wasa da dokoki.
A karshe, bayanin ya jaddada cewa, kasar Sin tana da kwarin gwiwa sosai wajen ba da kariya ga ikon mallakar yankin kasa da yankin teku na Sin. Kome yunkurin keta ikon Sin a wannan fanni ta hanyar yanke hukunci ba bisa doka ba ba zai cika ba. A ko da yaushe kasar Sin tana share fagen kiyaye iko da moriyarta ta mallakar yankin kasa da na teku, kuma wannan ne alhakin dake bisa wuyanta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya shiyya da ma duniya baki daya.(Fatima)