in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata a rika sa in sar siyasa a yankin tekun kudancin Sin ba
2016-06-09 13:10:31 cri

A kwanan baya, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Amurka ya ba da labari cewa, kakakin ofishin Zhu Haiquan ya aika wata wasika mai lakabin "Bai kamata a rika sa in sar siyasa a yankin tekun kudancin Sin ba" ga jaridar New York Times, inda ya bayyana matsayin da kasar Sin ke dauka kan batun tekun kudancin kasar, tare kuma da mai da martani ga sharhin da wannan jarida ta wallafa game da "yin gasar jaruntaka a yankin tekun kudancin Sin", inda ya jaddada cewa, bai kamata a yi gasar siyasa a yankin tekun kudancin Sin ba.

Mr. Zhu ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, kasar Sin ta kare ikonta a yankin tekun kudancin kasar ne domin kiyaye 'yancinta bisa doka. Bayan yakin duniya na biyu, kasar Sin ta sake rike ikon mallakar jerin tsibiran Nansha da na Xisha bisa sanarwar Alkahira da sanarwar Potsdam. Amma tun daga shekarun 70 na karnin da ya wuce, wasu kasashe sun fara neman mallakar wasu tsibiran Nansha ba bisa doka ba.

A game da haka, Mr. Zhu ya bayyana cewa, hanya daya tak da za a cimma burin daidaita batun tekun kudancin Sin ita ce yin shawarwari a tsakanin kasashen da wannan batu ya shafa. Ya kara da cewa, kasar Sin tana yin hakuri a yayin da take kokarin daidaita batun ta hanyar diplomasiyya. Ya kuma jaddada cewa, bai kamata a mai da yankin tekun kudu a matsayin wurin yin gasar siyasa ba. Muna fatan kasar Amurka za ta daina nuna karfin sojanta, a maiamkon haka ta taka rawa mai yakini wajen inganta shawarwari.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China