Tambayar wani dan jarida cewa, ministan tsaron kasar Amurka Ashton Carter da jami'in hukumar tsaro ta kasar Japan sun ba da jawabai a gun taron Shangri-La, wadanda suke da nasaba da batun tekun kuducin kasar Sin, inda kuma suka nuna yatsa ga kasar Sin. A game da haka, mane ne ra'ayinki?
Madam Hua ta amsa cewa, kasar Sin ta san jawaban da jami'an tsaro na kasar Amurka da na Japan suka yi, kuma abin da suka bayyana ba shi da gaskiya, sun shafa kashin kaza ga ayyukan gine-gine a tsibiran teku da kasar Sin ta yi bisa doka, kuma tare da nufin janyo sabani a tsakanin Sin da kasashen dake makwabtaka da ita. Kasar Sin ta nuna adawa da haka, don haka tawagar wakilan kasar Sin dake halartar taron sun riga sun mai da martani gare su da kuma bayyana ra'ayin kasar Sin. Ta kuma jaddada cewa, na farko, kasar Sin tana da ikon mulki kan jerin tsibiran Nansha da kuma yankunan tekun dake kewayansu, hakikanin tarihi ya iya shaida haka. Na biyu, kasar Sin ta gudanar da ayyukan gine-gine a tsibiranta, hakan bai karya dokokin kasa da kasa ba. Na uku, kasar Philippines ta gabatar da kara kan batun tekun kuducin kasar Sin ne, don neman musunta ikon da kasar Sin take da shi a kan tsibiran tekun kuducin kasar a maimakon kawar da sabani. Na hudu, a game da ka'idar da aka tsara, kasar Sin da kungiyar kasashen dake kudu maso gabashin Asiya ASEAN sun fitar da sanarwar da ta shafi bangarori daban daban dangane da tekun kuducin kasar Sin. Wannan sanarwa ta zama ka'ida ta wannan shiyya, ya kamata bangarori daban daban su bi wannan ka'ida yadda ya kamata.(Lami)