in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jinjinawa wasu kasashe da mutane da suka bayyana ra'ayinsu kan batun tekun kudancin Sin
2016-06-06 20:04:00 cri
A yau Litinin ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin ta jinjinawa kasashen Tanzaniya, Uganda, Eritrea, Comoros da kuma mataimakin shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka wajen bayyana ra'ayoyinsu kan batun tekun kudancin Sin.

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, kasashen Tanzaniya, da Uganda, da Eritrea, da Comoros, da mataimakin shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka da sauransu suka nuna goyon bayansu ga matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun tekun kudancin kasar. Mafi yawan kasashen duniya ba su goyi bayan matakin shari'a da Philippines ta dauka kan batun maimakon neman yin sulhu, kuma suna ganin cewa, kamata ya yi Philippines ta yi shawarwari da Sin domin daidaita wannan batu.

Game da wannan batu, Hong Lei ya furta cewa, kasashen Tanzaniya, Uganda, Eritrea, Comoros da kuma mataimakin shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka sun bayyana ra'ayinsu cikin adalci, hakan ya dace da hakikanin yanayin da ake ciki kan batun tekun kudancin Sin, tare da wakiltar muryoyin kasashen duniya masu adalci. Kuma Sin ta jinjina musu. A sa'i daya, ta kalubalanci kasar da abin ya shafa da ta bi yarjejeniyar da ta daddale da Sin da matsaya daya da aka cimma a wannan yanki, ta kuma kama hanyar da ta dace ta daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China