in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha: yin katsalandan a batun tekun kudancin kasar Sin zai tsananta halin da ake ciki
2016-06-11 13:11:05 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana a jiya Jumma'a cewa, kasar Rasha ta yi imani da cewa, idan sauran kasashe suka sanya baki kan batun tekun kudancin kasar Sin, tabbas halin da ake ciki a yankin zai kara tsananta.

Bisa labarin da aka bayar a kan shafin internet na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha, an ce, Maria Zakharova ta kira taron manema labarai a wannan rana cewa, kasar Rasha tana ganin cewa, yanayin yankin tekun kudancin kasar Sin na haifar da tasiri sosai ga tsaro da zaman lafiya a yankin Pacific na nahiyar Asiya, idan sauran kasashe suka nemi sa baki kan batun, tabbas halin da ake ciki a yankin zai kara tsananta.

Ta kuma kara da cewa, kasar Rasha ta yi imani da cewa, ya kamata kasashe daban daban da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa su bi ka'idar kaucewa yin amfani da makamai, da ci gaba da kokarin daidaita batun ta hanyar diplomasiyya bisa yarjejeniyar teku ta MDD da sanarwar bangarori daban daban na yankin tekun kudu da kuma sauran ka'idoji. Ban da haka kuma, kasar Rasha ta ce, ya kamata bangarori daban daban su yi shawarwari don tattaunawa kan wannan batu kai tsaye.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China