in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta nuna goyon baya ga matsayin da Sin ta dauka kan batun tekun kudancin kasar
2016-06-23 11:18:52 cri
A jiya Laraba 22 ga wata, ta bakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ba da sanarwar cewa, tana nuna goyon baya ga matsayin da Sin ta dauka kan batun tekun kudancin kasar.

Sanarwar ta ce, kasar Afirka ta Kudu tana mai da hankali sosai kan yunkurin mayar da batun tekun kudancin kasar Sin na siyasa a duniya.

Kuma sanarwar ta kara da cewa, kasar ta nuna goyon baya ga kasashen dake da alaka da wannan batu kai tsaye da su yi shawarwari tsakaninsu ta hanyar girmamawa tarihi da bin dokokin duniya, domin daidaita wannan batu tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudu.

Kasar Afirka ta Kudu tana ganin cewa, kamata ya yi kasa da kasa su nuna goyon baya ga duk kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta shiyya shiyya.

Kafin wannan, kasashen Kenya, Tanzaniya, Zambiya, Kamaru, Habasha, Lesotho, Malawi da wasu sauran kasashen Afirka sun nuna fahimta da goyon baya kan matsayin da kasar Sin ta dauka game da wannan batu a wurare daban daban.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China