A yau ranar 23 ga wata, an fara zaben jin ra'ayoyin jama'ar Birtaniya game da janyewa ko a'a daga EU. An fara gudanar da kada kuri'un a tassoshin zabe dake wurare daban daban na kasar tun daga karfe 7 na safe a wannan rana, kuma 'yan Burtaniya din zasu bada ra'ayinsu kan kasancewar kasarsu ko a'a a cikin kungiyar EU.
Bayan da aka fara yakin neman zabe, an samu bangarori biyu tsakanin masu goyon bayan tsayawar Birtaniya a EU da kuma masu neman ficewa daga EU wanda kuma tazarar dake tsakaninsu bata da yawa sosai .
Gidan rediyo na kasar Birtaniya wato BBC ya yi nazari kan kididdigar da hukumomin binciken ra'ayoyin jama'ar kasar suka yi kuma ya nuna cewa, yawan mutanen da suka nuna goyon baya ga janyewa daga kungiyar EU ya kai kashi 45 cikin dari, wanda ya wuce na masu goyon bayan kasancewar kasar a EU da kashi 1 cikin dari.
Masana na ganin cewa, sakamakon zaben zai yi babban tasiri ga dangantakar dake tsakanin Birtaniya da EU har ma yanayin siyasa na kasar Birtaniya. (Zainab)