A yayin taron, wanda za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen musulmi su hada kai ba tare da samun Baraka ba. Sannan ya sanar da cewa, za a kafa wata Cibiyar hadin gwiwar addinin musulunci da jami'an 'yan sanda a Istanbul, don yaki da ta'addanci yadda ya kamata. (Bilkisu)