in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen saman yakin Turkiya sun yi luguden wuta kan dakarun PKK a arewacin Iraki
2016-04-06 13:27:26 cri
Ofishin hafsan hafsoshin sojojin kasar Turkiya ya bayar da sanarwa a ranar 5 ga wata, cewa sojojin saman Turkiya sun kai hari ta jiragen yaki kan dakarun Kurdistan PKK a arewacin kasar Iraki.

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin saman Turkiya sun tura jiragen yaki 8 don kai harin kan dakarun PKK dake arewacin kasar Iraki, wanda ya taimaka wajen lalata wurare da dakunan ajiye makamai na mayakan PKK. Amma sanarwar ba ta bayyana yawan mutanen da suka mutu ko raunata a sakamakon harin ba.

A kwanakin baya, an sha fuskantar hare-haren ta'addanci a kasar Turkiya, lamarin da ya sanya gwamnatin kasar zafafa yakinta da dakarun PKK dake kudu maso gabashin kasar, tare da kama mutanen dake da alaka da kungiyar IS da sauran kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a wurare daban daban na kasar, da kuma kara sa ido kan yankin iyakar kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China