in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'YANCIN RATSA SASSAN TEKUN KASAR SIN, AMURKA NA DA IKON YIN HAKA BISA DOKA KO DAI GWAJIN KARFIN TUWO NE?
2016-06-03 20:40:54 cri
Batun ikon ratsa sassan tekun kudancin kasar Sin, batu ne da ya dade yana daukar hankalin kasashen duniya, musamman ganin yadda masharhanta suka dade suna bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da hakan. Sai dai abun lura a nan shi ne yadda Amurka ke maida kan ta tamkar alkali, dake da iko na doka wajen tabbatar da ra'ayin ta kan wannan batu, tare da daukar matsaya biyu kan matakan da ya dace a bi wajen warware takaddamar da ta dabaibaye wannan lamari.

Cikin wadanda suka bayyana ra'ayin su, game da matakan baya bayan nan da Amurka ta dauka hadda wata matashi mai suna Oh Beigong, wadda ke zaune a Taipei dake Taiwan. Wadda cikin mamaki ta nuna baiken ta, game da yadda kwamandan sojojin ruwan Amurka Admiral Harry B. Harris, ya bada umarni ga wasu jiragen ruwan yaki na Amurka, suka kutsa kai cikin sassan yankin ruwan da kasar Sin ke mallaka, duk kuwa da cewa yana sane kasar Sin ta dade da tabbatar da ikon mallakar wannan yanki mai kunshe da tsibirai.

Wani bangare na wasikar matashiyar wadda mahaifinta masunci ne, cikin shagube ta bayyana cewa " Na rubuta wannan wasika gare ka ne domin na taya ka murnar amfani da dokokin da suka bada dama, ga sojojin ruwa su yi amfani da jirage domin shawagi a ruwaye na kasa da kasa. Ka nuna karfin hali, ganin yadda a ranar 10 ga watan Mayu, ka tura wasu manyan jiragen sojin ruwa zuwa daf da wasu tsibirai da tun tsawon lokaci ke karkashin ikon kasar Sin.

Cikin wannan wasika da matashiyar ta aike da kwafin ta ga sakataren Amurka mai kula da harkokin sojin ruwa Ray Mabus, da sakataren tsaron kasar Ashton Carter, da kuma firaministan kasar Japan Shinzo Abe, ta zayyana irin hadarin dake tattare da wannan mataki da Amurka ta dauka, tana mai cewa jami'an da suka ba da umarnin aiwatar da wannan kutse, sun jefa rayukan dakarun su cikin hadari, ba tare da nuna wata damuwa ba.

Ta ce "Ka yi karfin hali wajen sanya rayukan sojojin ruwan ka cikin hadari, domin ba ka da tabbaci game da ko kasar Sin za ta kyale wadannan jirage ko a'a. Ga misali akwai karon batta da ya auku, tsakanin daya daga cikin jiragen ku na leken asiri mai lamba EP-3, da jirgin yakin Sin mai lamba J8 a ranar 1 ga watan Afirilun shekarar 2001, a wancan lokacin ma ba wanda ya yi zaton hakan za ta auku, kuma aukuwar hakan ta sabbaba mutuwar sojin kasar Sin Laftana kwamanda Wang Wei, wanda daga bisani kasar Sin ta karrama, bisa matakin da ya dauka na kare ikon yankin kasar sa".

Marubuciyar wasikar ta kara da cewa, "Hakika Amurka na wuce gona da iri, tana kuma rufe idanun ta daga abin da ka je ya zo, ganin yadda a baya irin wannan mataki da take dauka, kan janyo tashin hankali maras dalili. Ga misali cikin shekarun 1980, jirgin ruwan yakin tarayyar soviet ya taba karo gaba da gaba da na Amurka, bayan da Rashan ta zargi Amurka da ratsa yankunan dake karkashin ikon ta ba bisa ka'ida ba. A yanzu ma da yawa daga masharhanta na ganin mai zai hana Sin ta dauki irin wannan mataki, kan jiragen ruwan na Amurka dake kutse a yankuna da tsibiran dake karkashin ikon ta".

Wannan dai ba shi ne karon farko da Amurka ta keta hurumin kasar Sin game da ikon kare yankunan ta ba, inda ko da a cikin watannin Janairu da Oktobar da suka shude, ta gudanar da kutse cikin yankunan da ake takaddama a kan su.

Ko shakka ba bu wannan tsokana ce karara. Kuma a cewar marubuciyar wannan wasika, "idan har Sin ta dauki matakin soji, mazauna yankunan ne za su fada cikin mawuyacin haki". Ta kara da cewa "Mai zai sanya mu fadawa masifa sakamakon abun da Amurka ke son aikatawa, duk kuwa da cewa bisa doka ba ta da ikon yin hakan. Shin ba ka jin wani abu a ranka? game da a koda yaushe kasar ka ta Amurka na nuna wa duniya cewa Sin ce kadai ke da laifi cikin dukkanin kasashen da ke takaddama kan wadannan yankuna da tsibirai?

Sanin kowa ne dai kasar Sin ba ta taba hana wata kasa ikon ratsa yankunan ruwa da dokokin kasa da kasa suka bada izinin amfani da su ba.

Game da zargin mamayar yankuna da Amurkan ke wa kasar Sin kuwa, babban abun tambaya shi ne, me yasa Amurkan ba ta nuna dan yatsa kan jibge dakaru da mahukuntan yankin Taiwan suka yi a tsibirin Taiping wanda Philippines ke cewa na ta ne ba?

Magana ta gaskiya ita ce Amurka na daukar matakai ne kawai na dakile tasirin da take ganin kasar Sin na iya yi, ko kaucewa yin takara da Sin a harkokin da suka shafi kasa da kasa. Don haka bai dace Amurka ta rika nunawa duniya cewa ita kasa ce mai burin wanzar da da'a, ko biyayya ga dokokin kasa da kasa ba, tun da dai a zahiri take cewa Amurkan na amfani da matsaya biyu, ta kuma zama tamkar bakin-ganga wajen sauya matsaya, da kaucewa adalci kan batun yankuna, da tsibiran dake wannan yanki na kudancin kasar Sin. (Leslie Fong, tsohon edita na jaridar "The Straits Times" ta Singapore)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China