Kasashen Afirka uku sun nuna goyon baya ga kasar Sin kan batun tekun kudancin Sin
Jiya Laraba 15 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Habasha Taye Astkesilassie ya gana da jakadan kasar Sin dake kasar La Yifan, domin yin musayar ra'ayoyi kan wasu batutuwan dake janyo hankulansu, haka kuma, a yayin ganawar tasu, bayan ya ji cikakken bayani kan tarihin batun tekun kudancin kasar Sin da jakadan kasar Sin ya yi masa, Mr. Taye Astkesilassie ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Habasha ta gane da kuma nuna goyon baya game da matsayin kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar, kana, kasarsa tana fatan kasashen da abin ya shafa za su warware wannan matsalar ta hanyar yin shawarwari bisa yarjejeniyar da suka taba kullawa da kuma ra'ayin daya da aka cimma a wannan yanki a baya, sabo da zaman lafiya da zaman karko a tekun kudancin kasar Sin na da muhimmiyar ma'ana wajen tabbatar da moriyar kasashen da abin ya shafa.
A nasa bangare kuma, shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ya bayyana a yayin ganawarsa da jakadan kasar Sin dake kasar Wang Shiting a ran 14 ga wata cewa, kasarsa na lura da yanayin tekun kudancin kasar Sin, kuma Malawi na goyon bayan matsayin kasar Sin kan wannan batu.
Ya ce, tare da sauran kasashen nahiyar Afirka, kasar Malawi tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su iya warware sabaninsu ta hanyar zaman lafiya da kuma yin shawarwari, a maimakon neman janyo rikici.
Dadin dadawa, a yayin ganawa da Mr. Sun Wei mukaddashin jakada na wucin gadi na kasar Sin dake kasar Kamaru, wakilin da matsayinsa ya yi daidai da ministan harkokin wajen kasar Kamaru ya bayyana cewa, gwamnatin kasar tana maraba da bangarorin da abin ya shafa su warware sabanin dake tsakaninsu kan tekun kudancin kasar Sin ta hanyar yin shawarwari. (Maryam)