in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen da batun tekun kudancin Sin ya shafa sun yi shawarwari kai tsaye, in ji Uganda
2016-05-30 19:12:52 cri
Ministan harkokin wajen kasar Uganda Okello Oryem, ya bayyana cewa kasar Uganda na goyon bayan kasashen da batun takun kudancin Sin ya shafa wajen ganin sun gudanar da shawarwari kai tsaye, bisa yarjejeniyar da bangarorin suka kulla kan batun, domin warware matsalar ta hanyoyin zaman lafiya.

Kaza lika, Mr. Oryem ya ce, karar da kasar Philippines ta gabatar game da Tekun Kudancin Sin, ba za ta yi amfani ba wajen warware wannan matsala yadda ya kamata. Kaza lika gudanar da shawarwari kai tsaye a tsakanin kasar ta Philippines da kasar Sin ita ce hanyar da ta fi dacewa, wajen warware sabanin dake tsakaninsu game da tekun na Nanhai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China