Chen Xufeng da Mwencha sun tattauna ayyukan hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu ta fannonin raya hanyoyin jiragen kasa da motoci da jiragen sama da raya masana'antu a kasashen Afirka da kafa cibiyar kula da cututtuka ta Afirka.
Mwencha ya nuna yabo ga Sin kan gudummawar da ta samar da kuma sabon sakamakon hadin gwiwar da bangarorin biyu suka cimma, yana mai imanin cewa, bangarorin biyu za su kara zurfafa dangantakar hadin gwiwar.
Game da batun tekun kudancin kasar Sin, Mwencha ya nuna goyon baya ga matsayin Sin kan wannan batu, kana ya yi kira ga kasashen da abin ya shafa kai tsaye da su samar da damar yin shawarwari da juna, da warware matsalar ta hanyar yin shawarwari cikin lumana bisa dokokin kasa da kasa. Mwencha ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen da abin ya shafa da su bi ka'idojin sanarwar bangarori daban daban da batun tekun kudancin Sin ya shafa,tare da warware matsalar ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, da kara yin imani da juna, a kokarin tabbatar da zaman lafiya a tekun kudancin kasar Sin. (Zainab)