Yayin ganawar sa da shugaba Putin, Zhang Dejiang ya bayyana cewa, makasudin ziyararsa a wannan karo shi ne aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen Sin da Rasha suka cimma daidaito a kan su, da inganta hadin gwiwar dake tsakanin hukumomin tsara dokoki na kasashen biyu, da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin su a dukkan fannoni, don samun bunkasuwa da farfadowa tare.
A nasa bangare, Putin ya bayyana cewa, kasar Rasha ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar abokantaka tsakanin ta da Sin a dukkan fannoni, kana yana fatan za a kiyaye mu'amalar dake tsakanin sassan biyu, da kuma marawa juna baya, da fadada hadin gwiwa don daga dangantakar kasashen zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)