in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe gomai na goyon bayan matsayin Sin kan batun tekun kudancin Sin
2016-06-22 10:57:42 cri

Kasashe gomai sun bayyana goyon bayansu kan matsayin kasar Sin kan takadamar tekun kudancin Sin, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Hua Chunying.

Madam Hua ta yi watsi, a yayin wani taron manema labarai, kan bayanan dake nuna cewa, kawai kasashe takwas ne suka goyi bayan kasar Sin kan wannan batu, tare da kara cewa, "Na sani cewa, wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suna kasa bambanta fari da baki, amma ban yi tsammanin za su iya samun matsala kan adadi ba."

A halin yanzu kasashen dake goyon bayan kasar Sin na ci gaba da karuwa bayan da suka fahimci batun, in ji madam Hua, tare da nuna cewa, a baya bayan nan kasashen Zambiya, Kamaru, Habasha da Malawi sun kara yawan kasashen dake goyon bayan kasar Sin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China