A yayin da shugaba Mugabe ke zantawa da mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Zhang Ming a birnin Harare, ya ce, Zimbabuwe ta nuna cikakken goyon bayan ta ga matsayin da kasar Sin ke dauka a kan batun tekun kudancin kasar Sin, wato kamata ya yi kasashen da abin ya shafa su daidaita gardamar ta hanyar yin shawarwari cikin ruwan sanyi.(Lubabatu)