in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu jami'an kasar Afirka ta Kudu : Bai kamata ba kasashen ketare su tsoma baki cikin batun kudancin tekun kasar Sin
2016-06-17 20:36:17 cri

Kwanan baya, sashen kula da harkokin hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gayyaci tawagar bincike ta jami'an jam'iyyun kasashen ketare, a yayin da wasu daga cikinsu ke zantawa da manema labaru sun bayyana cewa, ya kamata a warware batun tekun kudancin kasar Sin ne ta hanyar yin tattaunawa a tsakanin kasashen da batun ya shafa, bai kamata kasashen ketare su shiga cikin lamarin ba.

Mamban kwamitin zartaswa na jam'iyyar ANC ta kasar Afirka ta kudu, kuma mamban kwamitin kula da harkokin ketare Ebrahim Ismail ya nuna cewa, akwai shaidun da suka nuna cewa, batutuwan da suka shafi kasashen Afirka, batutuwa ne da za a warware su a nahiyar Afirka, shiga lamarin da kasashen ketare suka yi ya kan haifar da rikici.

A saboda haka, ya kamata kasashen da batun ya shafa su warware rigima da matsaloli game da batun kudancin tekun kasar Sin ta hanyar yin shawarwari a tsakaninsu kai tsaye, kasashen ketare ba su da ikon shiga cikin wannan batu.

Babbar ma'ajin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Afirka ta kudu Joyce Moloi-Moropa ta bayyana cewa, kasarta ma na kula da batun kudancin tekun kasar Sin sosai, kuma ta fahimci cewa, kasar Sin tana fatan warware wannan batu ta hanyar lumana, kuma wannan mataki na Sin ya yi dai dai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China