in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Rasha Putin
2016-06-24 10:18:02 cri

A jiya Alhamis 23 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaran aikinsa na kasar Rasha Vlładimir Putin a birnin Tashkent dake kasar Uzbekistan.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yayin da aka cika shekaru 15 da daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin Sin da Rasha da cika shekaru 20 da kulla dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu, ziyarar da Putin zai kaiwa kasar Sin tana da babbar ma'ana. Sin tana son yin kokari tare da kasar Rasha wajen sa kaimi ga hadin gwiwar shimfida manufofin raya kasashen biyu, da hada shirin "ziri daya da hanya daya" da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya, da kuma yin mu'amala kan harkokin kasa da kasa da yankuna.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana son yin kokari tare da kasar Rasha wajen taimakawa raya kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaba Putin ya nuna jajantawa game da mutuwa da raunatar mutane da dama tare da hasarori a sakamakon mahaukaciyar guguwa da ta faru a lardin Jiangsu na kasar Sin, ya ce, kasashen biyu suna fahimtar juna da nuna goyon baya ga juna.
Shugaban Rasha zai kawo ziyara a kasar Sin, yana sa ran zai yi shawarwari tare da shugaba Xi Jinping kan raya dangantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China