Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Rasha Vlładimir Putin a birnin Ufa na kasar Rasha a jiya Laraba. Wannan ne dai karo na biyu da shugabannin suka gana da juna a bana.
Yayin tattaunawarsu, shugaba Xi ya yi nuni da cewa a watan Mayun bana, shi da shugaba Putin sun gana a birnin Moscow, inda suka tsaida kudurin hada zirin tattalin arziki na hanyar Siliki, da kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya. Kaza lika sun amince da batun bunkasa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin zuba jari, da na hada-hadar kudi, da makamashi, da samar da ababen more rayuwa kamar jiragen kasa mafiya sauri, da jiragen sama da sararin samaniya, da raya yankin Gabas mai nisa da sauransu.
Gwamnatocin kasashen biyu suna kuma aiwatar da manufofin hadin gwiwa da aka cimma daidaito a kan su, sun kuma samu sakamako mai gamsarwa a wasu sabbin fannoni.
A nasa bangare, Putin ya bayyana cewa, ana ci gaba da raya dangantakar abokantaka a tsakanin Rasha da Sin a dukkan fannoni. Kuma bangarorin biyu na mu'amala sosai a fannoni daban daban, suna kuma kiyaye hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa. Kaza lika dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu ta kara samun tagomashi. (Zainab)