A yayin taron, Li ya bayyana cewa, ziyarar aikin da shugaba Xi ya kai a Uzbekistan, da halartar taron kolin kungiyar SCO da ya gudana a Tashkent, muhimman ayyukan harkokin waje ne da kasar Sin ta yi a Uzbekistan da yankin tsakiyar Asiya baki daya, wadanda suka jawo hankulan kasashen Sin da Uzbekistan har ma da kasashen duniya kwarai. A cikin sa'o'i fiye da 20, shugaba Xi ya halarci bukukuwa fiye da 10, baya ga yin cudanya da takwaransa na Uzbekistan Islam Karimov, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, hadin kai a tsakaninsu a fannoni daban daban da kuma batutuwan duniya da na shiyya shiyya dake jawo hankulansu, sun kuma cimma ra'ayi daya. Ana iya cewar, an cimma gagarumar nasara a wannan ziyara. (Bilkisu)