in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma matsaya daya kan batun tekun Kudancin kasar tare da kasar Rasha
2016-04-29 20:46:13 cri

A yau Jumma'a ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov wanda ke ziyara a nan kasar Sin, inda Wang Yi ya gabatar da matsayin kasar Sin game da batun tekun Kudancin kasar.

Sergei Lavrov ya bayyana cewa, ya kamata a daidaita batun tekun Kudanicn kasar Sin ta hanyar yin shawarwari a tsakanin kasashen da batun ya shafa, kuma bai kamata sauran kasashe su tsoma baki a cikin lamarin ba.

Ban da haka kuma, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun cimma muhimmin matsayi cewa, ya kamata kasashen da abin ya shafa daidaita batun tekun Kudancin kasar Sin ta hanyar yin shawarwari kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, kuma ya kamata kasashen duniya musamman ma kasashen da ba su cikin yankin tekun Kudancin kasar Sin su taka rawa mai yakini kan yunkurin kiyaye zaman lafiya a yankin, a maimakon haddasa rikici .(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China