A cikin sharhin mista Cui ya nuna cewa, muhimmin abu kan batun tekun kudancin Sin shi ne takaddama kan yankin kasa da ikon mallakar teku. Abubuwan da kasar Sin ke yi na da nufin kiyaye 'yancinta kan yankin kasa da moriyarta kan teku. Sakamakon wasu maganganu da yadda Amurka ta ke jibge sojoji a kwanan baya ne ya kara tsanantar halin ake ciki a yankin. Idan ba a daina furta irin wadannan maganganu ba, to gaskiya komai yana iya faruwa a yankin, wanda babu wanda ke fatan ganin haka.
Bayan haka kuma, Cui ya bayyana a cikin sharhin cewa, kasar Sin na girmama kasancewar Amurka a yankin Asiya da Pacifik tun fil azal, da kuma moriyarta ta halal a yankin, amma wasu mutane na musanta karuwar halaccin ikon kasar Sin da moriyarta a yankin.
Bugu da kari, Cui ya jaddada a cikin sharhin cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na da muhimmanci kwarai, don haka ba za mu yarda ta lalace sakamakon batun tekun kudancin Sin ba. Mai yiwuwa ne bangarorin biyu suna da wasu bambance-bambance masu muhimmanci a wasu fannoni, amma duk da haka suna da moriya bai daya. A saboda haka, bai kamata kasashen biyu su ci gaba da ja-in-ja a kan batun tekun kudancin Sin ba. (Bilkisu)