Nahuta Abubakar, mai shiga tsakani na hukumar daidaita harkokin gaggawa ta Nigeria (NEMA) ya gaya wa wakilinmu cewa, 'yan gudun hijira sama da 5000 sun yi rajista, ciki har da yara 100 dake fama da karancin abincin gina jiki.
Wasu 'yan gudun hijira suna zama a wuraren da aka tsugunar da su, yayin da wasu suke zama a makarantu da hukumomi da sauransu.
Wadannan 'yan gudun hijira, wasu daga cikinsu sun zo daga Bosso da Diffa ta kasar Nijer, yayin da wasu suka zo daga jihohin Yobe da Borno na Nigeria.(Fatima)