in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani bam da ya tashi a wata mota ya kashe mutane 6 a arewa maso gabashin Nigeria
2015-01-01 16:02:53 cri
Wani bam da ya haifar da asarar rayukan mutane 6 ya fashe a wata mota a kusa da rumfar jami'an tsaro dake bincike a kan hanyar jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nigeria.

Hukumomin 'yan sanda sun ce, bam din wanda ke boye a cikin motar ya fashe ne a garin Fika a yayin da motar ke tafiya a kan hanya.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Yobe, Marcus Danladi ya ce, mutane 6 dake cikin motar su kadai ne suka rasa rayukansu.

Danladi ya ce, jami'an tsaro sun tashi haikan domin tabbatar da kariyar jama'a, musamman saboda jama'a na fargabar karin aukuwar hare-hare a yankin na gabashin kasar da kuma Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe,inda a kwanan nan ne aka kaddamar da wani hari a garin.

Jihar ta Yobe na daga cikin johohin Nigeriya 3 dake arewa maso gabashin kasar wadanda shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci.

Ita jihar Yobe tana iyaka da Borno da Adamawa inda aka kafa dokar ta baci saboda 'yan kungiyar Boko Haram sun yi kaka gida a yankunansu.

Kungiyar 'yan tsageran Boko Haram na ci gaba da kasancewa barazana a kan lamurran tsaro na kasar ta Nigeria. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China