A cewar jami'in hulda da dama'a na rundunar Birgediya Janar Olajide Laleye, sabbin matakan da rundunar ke dauka a baya bayan nan, sun haifar da kyakkyawan sakamako, musamman a yankunan arewa maso gabashin kasar.
Laleye ya kara da cewa, za a baiwa daukacin jami'an da za su rika aiki a wannan yanki horo na musamman a fannin yaki da ayyukan ta'addanci kafin su fara aiki.
A wani ci gaban kuma, rundunar sojin dake ayyukanta a jihar Borno ta bayyana kafa dokar takaita zirga-zirgar ababen hawa ta kwanaki 2, a birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar, dokar da za ta shafi kwanakin hutu na shagulgulan Maulidi da al'ummar musulmi ke gudanarwa a kowace shekara.
Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriyar ta ware ranekun Alhamis da Jumma'a a matsayin ranekun hutun bikin na Maulidi. (Saminu Hassan)