in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 4 sun mutu lokacin da wata jirgi mai saukar ungulu ta fadi a Nigeria
2015-08-13 09:25:15 cri
Rahotanni daga tarayyar Nigeriya ya tabbatar da cewar mutane 4 ne suka hallaka a yankin Oworonshoki a jihar Ikko dake kudu maso yammacin kasar bayan da wani jirgi mai saukan ungulu mallakar rukunin Bristow na kasar Amurka ya fadi.

A wannan lokacin tana dauke da mutane 12 kuma 6 daga cikin su a samu ceto su da rayukan su baya ga wassu guda 2 da har yanzu ake kan neman su kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandar jihar Patricia Amadin ta tabbatar.

Jirgin ya fada cikin teku ne dake kusa da gadar 3rd mainland wanda ya hada tsibirin jihar da cikin gari.

Ibrahim Farinloye kakakin hukumar bada agajin gaggawa na kasar wato NEMA a jihar ta Ikko ya shaida ma Xinhua cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 3 na rana kuma mutane 4 an tabbatar da mutuwar su a cikin hadarin, da hukumar kula da tashin jiragen sama ta kasar NCAA ita ma ta tabbatar.

A cikin wata sanarwa daga hukumar NCAA da kakakin ta Fan Ndubuoke ya sanya ma hannu, ya ce jirgin mai saukar ungulu na rukunin Bristow yana kan hanyar shi ne daga daya daga cikin rijiyoyin man kasar zuwa Ikko kuma ana tsammanin isowar shi da misalin karfe 3 da minti 35 na yammacin wannan rana sai dai har yanzu ba su tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukan su ba tukuna.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China