A daren ranar 20 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar maraba da shugaban kasar Poland Andrzej Duda ya shirya a fadar sarki dake birnin Warsaw.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Poland tana daya daga cikin kasashen jerin farko da suka amince da kafa dangantakar diplomasiyya da kasar Sin, wadda ta samar da gudummawa da goyon baya ga raya sabuwar kasar Sin, don haka jama'ar kasar Sin ba za su manta da wannan ba. A halin yanzu, kasashen biyu sun kara yin imani da juna a fannin siyasa, da raya hadin gwiwarsu ta samun moriyar juna, da yin mu'amala da juna a fannoni daban daban, ta haka za a kawo babbar moriya ga kasashen biyu da jama'arsu.
A nasa bangare, shugaba Agata Kornhauser-Duda ya bayyana cewa, ko da yake Poland da Sin suna da nisa, amma sun sada zumunta cikin dogon lokaci. A karnin 21, shirin "ziri daya da hanya daya" da Sin take jagoranta ya kara samar da damar yin hadin gwiwa a tsakanin Poland da Sin. Kasar Poland tana son hada shirin samun bunkasuwa mai dorewa da shirin "ziri daya da hanya daya" waje guda, da kuma zurfafa hadin gwiwar bangarorin 2 a dukkan fannoni.
A jiya ranar 20 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Poland Beata Szydło da shugaban majalisar dattijai ta kasar Poland Stanisław Karczewski da kuma shugaban majalisar wakilan kasar Marek Kuchciński a birnin Warsaw. (Zainab)