Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wadda ta bayyana hakan yau yayin taron maname labarai a nan birnin Beijing, ta kuma ce Mr Li zai yi jawabi a bikin bude dandalin.
Ana kuma saran firaministan na kasar Sin zai gana da kusoshin gwamnati,mutumin da ya kirkiro dandalin na Davos Klau Scwab da sauran mahalarta dandalin.
Bugu da kari, firaminista Li zai tattauna da wakilai daga bangarori daban-daban wadanda suka hada da na kasuwanci, harkokin kudi,kungiyoyin masana da kafofin watsa labarai.
Kimanin wakilan daga bangarorin siyasa,masana'antu,masana da kafofin watsa labarai 1,700 ne daga kasashe sama da 90 ake saran za su halarci dandanlin na bana bisa taken "juyin-juya halin masana'antu karo na hudu da kuma tasirinsa".(Ibrahim)