Sanarwar ta jaddada cewa, yanzu ana ci gaba da yin bincike kan dalilin abkuwar hadarin, ba za a kawar da yiwuwar harin ta'addanci, matsalar fasahohi da dai sauransu ba.
A safiyar ranar 19 ga watan Mayu, jirgin saman samfurin MS804 na kamfanin EA da ya tashi daga birnin Paris zuwa Alkahira ya bace daga na'urar Radar a yayin da yake sararin yankin tekun Bahar Rum, tare da mutane 66. A ranar 20 ga watan Mayu, hukumar sojojin Masar ta sanar da cewa, masu aikin ceto sun gano wasu tarkacen jirgin saman da gawawwakin fasinjoji da kuma kayayyakinsu a yankin teku dake da tazarar kilomita 290 daga arewacin tashar ruwan Alexender ta kasar.(Fatima)