Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, an riga an mika bakin akwatin ga kwamitin bincike ta kasar Masar dake birnin Alexander na kasar, inda hukumar shari'ar kasar da kwamitin dake bincike kan hadari za su yi nazari kan bayanin da bakin akwatin cikin hadin gwiwa. A sa'i daya kuma, ana ci gaba da neman dayan bakin akwatin dake dauke da bayanan hanyoyin tafiyar jirgin saman da ya fadi. (Maryam)