in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang da Sherif Ismail sun aikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 60 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin kasashen su
2016-05-31 09:47:50 cri

A kwanakin baya ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaran aikinsa na kasar Masar Sherif Ismail suka aikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen su.

A cikin sakonsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, a cikin shekarun 60, kasashen biyu sun nuna goyon baya da girmamawa da yin imani da juna, an sada zumunta a tsakaninsu na dogon lokaci. Ya zuwa yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Masar ta kasance abin misali a dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa, da kasashen Afirka, da kuma tsakanin kasashe masu tasowa. A shekarun baya baya nan, an kiyaye raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma sun kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban. Kasar Sin tana son hada kai tare da kasar Masar don kara zurfafa zumunta da hadin gwiwarsu, ta yadda za su amfanawa jama'arsu.

A nasa bangare, Ismail ya bayyana cewa, kasashen biyu sun dade suna yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, don haka yana fatan kasashen za su inganta dangantakarsu, kana gwamnatocin kasashen biyu za su kiyaye hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta yaddda za ta kasance mai fa'ida ga jama'ar kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China