in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin dake kasar Masar sun gudanar da harkokin jin kai a watan Ramadan
2016-06-15 12:22:41 cri

A watan Ramadan, kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Sin dake Masar da hukumar jin kai ta kasar Masar sun gudanar da harkokin jin kai tare a kwanan baya.

A lokacin da ake gudanar da wannan aiki, kamfanoni 27 na kasar Sin dake kasar Masar da kungiyar cinikin kayayyakin duwatsu ta kasar Sin dake Masar sun tattara kudi Pound na Masar dubu 270, da samar da kayayyakin kyauta 1300. Sannan za su samar da abincin halal fiye da dari 400 a kowace rana cikin jerin kwanaki 20 masu zuwa.

A kwanan baya, jakadan kasar Sin dake kasar Masar Song Aiguo da kuma mashawarcin jakada kan harkokin kasuwanci Han Bing sun ba da abincin halal da abubuwan kyauta ga mutane.

Shugaban kungiyar neman bunkasuwa ta kasar Masar ya nuna godiya ga ayyukan jin kai da kasar Sin ta yi, ya bayyana cewa, hakan ya shaida cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan zaman rayuwar mutanen kasar Masar, kana ya bayyana zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

Kamfanonin Sin dake kasar Masar sun yi ayyukan jin kai a watan Ramadan karo na farko a shekarar bara, wannan karo ne na biyu da suka yi wannan ayyuka. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China