Ba za a iya kawar da yiwuwar harin ta'addanci game da faduwar jirgin saman Masar ba
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Faransa suka bayar a jiya Lahadi, masu bincike na kasar Faransa sun bayyana cewa, mai yiwuwa ne ko wane irin hasashen da aka yi game da dalilin faduwar jirgin saman nan mai lamba MS804, na kamfanin jiragen saman kasar Masar ya iya zama gaskiya, kana ba za a iya kawar da yiwuwar harin ta'addanci game da faduwar jirgin saman ba
Rahotannin na cewa ko da yake ba za a iya kawar da yiwuwar harin ta'addanci ba, amma mawuyaci ne a ce an yi amfani da fashewar bom. A halin yanzu, masu bincike suna ci gaba da nazarin halin saukar jirgin saman a filin jiragen sama dake Charles de Gaulle, da kuma dukkan mutanen da wata kila suke da nasaba da wannan jirgi. (Zainab)