An labarta cewa, ana shirin nuna kulawajanyo hankalin duniya ga harkokin da kasar Sin ke gudanarwa a tekun kudancinta a sanarwar da za a fitar a gun taron. Baya ga haka, a yayin da firaministan kasar Japan ke zantawa manema labarai tare da takwaransa na kasar Canada, ya bayyana matukar kulawarsa ga yadda kasar Sin ke gina tsibirai da gudanar da harkokin soja a yankin tekun. A game da hakan, kakakin Madan Hua ta bayyana cewa, kasar Japan ta jima da tana rura wuta a kakururuta n batun tekun kudancin kasar Sin. A yanayin da tattalin arzikin duniya da akeke ciki, kamata ya yi taron kolin G7 ya mai da hankali a kan gudanar da harkokin tattalin arziki da kuma hadin gwiwa. Amma a maimakon haka, kasar Japan a matsayinta na kasar da ke karbar bakuncin taron, tana kokarin shirya wani makirci bisa ga a taron, abin da ba zai amfana wa kungiyar G7 ba, balle ma a samu zaman lafiya a yankin tekun kudancin kasar Sin.(Lubabatu)