A yayin da yake mayar da martani ga kalamin Hagel, Mr. Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta amince, kuma ba za ta halarci zaman yanke hukunci kan batun da za a yi. Wannan ne matsayin da kasar Sin take dauka a kullum, kuma hakan a fili yake. Amma wasu 'yan siyasan Amurka sun rufe idonsu kan gaskiyar lamari da suka dade suna sane da ita, har ma suna tankwara dokokin kasa da kasa kamar yadda suke so domin yunkurin cimma burinsu na siyasa da ba sa iya gaya wa jama'a kai tsaye ba. A waje daya, Lu Kang ya nuna cewa, kasar Amurka ta kan yi amfani ko ta yi watsi da dokokin kasa da kasa domin biyan bukatunta kawai, don haka dole ne kasashen duniya su yi la'akari da irin wannan matsayin da kasar Amurka take dauka. (Sanusi Chen)