A 'yan kwanakin baya Jaridar 'Business Daily' ta kasar Nijeriya ta ruwaito wani rahoton asusun ba da lamuni na IMF da ke cewa, a cikin 'yan shekarun da suka shude, kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikaya da zuba jari da kuma ba da kudin taimako ga kasashen Afirka da ke kudu da Sahara. A ganin rahoton, bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya yi tasiri ga bunkasuwar wannan yanki.
Rahoton ya ce, duk wata karuwar kashi 1 bisa dari na zuba jari a kan kadarori da Sin ta samu, ya kan kara kayayyakin da wannan yanki da ke kudu da Sahara na Afirka yake fitar zuwa kasashen waje da yawansa ya kai kashi 0.6 bisa dari. Ana samun irin wannan sakamako ne ta hanyoyi biyu, na daya, cinikayyar kai tsaye a tsakaninsu, na biyu, jarin da Sin ta zuba ya yi tasiri ga bunkasuwar tattalin arziki da kasuwannin kayayyaki a duk duniya, sakamakon haka, Sin ta sa kaimi ga bunkasuwar yankin Afirka. A cikinsu kuma, kasar Sin ta fi sa kaimi ga bunkasuwar kasashen Afirka masu arzikin makamashi, musamman masu arzikin man fetur, sabo da wadannan kasashen sun fi fitar da kaya zuwa Sin.
Kididdigar gwamnatin kasar Nijeirya ta nuna cewa, kayayyakin Sin sun kai kashi 18.2 bisa dari na dukkan kayayyakin da Nijeriya ta shigo da su daga kasashen waje, sakamakon hakan Sin ta zama babbar abokiyar cinikkaya ta Nijeriya. Wasu mazanarta sun bayyana cewa, har zuwa yanzu Nijeriya ba ta amfana da kyakkyawar damar da Sin ta samar mata ba, Nijeriya tana bukatar gudanar da wasu ayyuka cikin gaggawa, wadanda suka hada da tsara shirin bunkasuwa a dukkan fannoni, da sa kaimi wajen dai-daita harkokin kere-kere, da horar da masu fasahohi, da dabarun zamani ga shugabannin kamfanoni da kwarewarsu ta shugabanci da dai sauransu.(Danladi)