Shugaban kwamitin sulhu na MDD a wannan karo, kana zaunannen wakilin Faransa a MDD, Francois Delattre ya gabatar da sanarwar a wannan rana, inda aka bayyana cewa, da babbar murya ce membobin kwamitin sulhu suka yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a wani gidan rawa na 'yan luwadi da madigo dake Orlando a ranar Lahadi 12 ga wata, tare da jajantawa iyalan wadanda suka mutu da kuma gwamnatin Amurka, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.
Dadin dadawa, sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya nanata cewa, kowane irin ta'addanci, barazana ce mafi tsanani ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Kuma ya zama wajibi ga kasashen duniya dasu yaki da ta'addanci bisa kundin tsarin mulkin MDD da dokokin kasa da kasa yadda ya kamata.(Fatima)