A wannan rana kuma, bayan ganawarsa da shugaban hukumar binciken bayanan sirrin ta FBI da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa, shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi a fadar White House cewa, ko da yake, yanzu ana mataki na farko wajen yin bincike kan wannan lamari, amma bisa labarin da gwamnatin kasar ta samu, ana iya tabbatar da cewa, wannan hari ne na ta'addanci da aka kaddamar domin nuna kiyayya.
Kaza lika, bisa labarin da aka samu, an ce, sunan maharin shi ne Omar Mateen mai shekaru 29, dan kasar Amurka ne wanda yake zaune a jihar Florida na kasar. Haka kuma, kafin faruwar wannan hari, ya taba bugawa 'yan sandan kasar waya ta 911, inda ya sanar da nuna biyayya ga kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS.
Bugu da kari, an ce, wannan harin bindiga shi ne mafi muni da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu yawa a tarihin kasar Amurka. (Maryam)