in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakatarorin harkokin wajen da na kudi na Amurka
2016-06-07 21:00:15 cri
A yau Talata 7 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da kuma na kudi, Jacob J.Lew a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, wadanda suke halartar taron shawarwari kan manyan tsare-tsare da tattalin arziki na Sin da Amurka karo na 8 da taron shawarwari tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka a fannin al'adu karo na 7.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, taruka biyu sun sami babban sakamako bisa kokarin bangarorin biyu. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su bullo da matakan da suka kamata a dauka, domin gaggauta kawo alheri ga jama'arsu.

A nasu bangare, John Kerry da Jacob J.Lew sun bayyana cewa, muhimmin jawabin da shugaba Xi ya gabatar a gun bikin kaddamar da tarukan biyu ya zayyana hanya mafi dacewa ga bangarorin biyu. Shugaban Amurka Barack Obama yana sanya ran ganawa da shugaba Xi a yayin halartarsa a taron koli na kungiyar G20 a watan Satumban bana a Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China