A wajen taron, babban sakataren kungiyar sa kaimi ga yin mu'amala a tsakanin kungiyoyin al'ummomin kasa da kasa ta kasar Sin You Jianhua ya yi jawabi a madadin kungiyar al'ummar kasar Sin, inda ya gabatar da sabuwar shawara kan tabbatar da hakkin dan Adam na duniya.
You Jianhua ya bayyana cewa, Sin tana fatan za a hada da ka'idojin tabbatar da hakkin dan Adam na dukkan jama'ar duniya da yanayin kasa da kasa.
You Jianhua ya kara da cewa, don sa kaimi ga tabbatar da hakkin dan Adam na duniya, kungiyar al'ummar kasar Sin ta ba da shawara a fannoni hudu, na farko, ya kamata a hada da aikin tabbatar da hakkin dan Adam da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta MDD ta shekarar 2030, musamman a dora muhimmanci ga ikon yin rayuwa na kasashe masu tasowa da na samun bunkasuwa.
Na biyu, ya kamata a duba sabbin nasarorin Sin da kasashe masu tasowa a fannin tabbatar da hakkin dan Adam, da nuna adawa ga aikin maida batun hakkin dan Adam a matsayin batun siyasa, da daukar ma'auni biyu kan batun.
Na uku, kamata ya yi kasa da kasa su dora muhimmanci ga hakkin 'yan gudun hijira, da batun nuna bambanci ga kabilu da sauransu.
Na hudu, kungiyar al'ummar kasar Sin tana son taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hakkin dan Adam na duniya. Yanzu kungiyar tana aiwatar da shirin sada zumunta a tsakanin al'ummomin Sin da Afirka don taimakawa jama'ar kasashen Afirka wajen kawar da talauci, da kiwon lafiyar mata da yara, kyautata yanayin ba da ilmi a makarantun firamare da midil da sauransu. (Zainab)