in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na yin garambawul ga rundunar sojojin kasar
2016-06-14 10:37:07 cri

Ministan tsaro na tarayyar Najeriya birgediya janar Mansur Dan-Ali ya fada cewar, ritayar da aka yi wa 38 daga cikin manyan jami'an sojojin kasar na daga cikin shirin garambawul da ake gudanarwa a rundunar sojin kasar.

Dan-Ali ya tabbatar da hakan ne a kwalejin horas da sojojin kasar dake birnin Abuja, ya kara da cewar, matakin bai kasance a matsayin cin zarafi ba ga dakarun kasar.

Ministan ya bukaci al'umma da kada su amince da duk wata jita-jita da ake yadawa game da ritayar da aka yi wa sojojin kasar kasancewar an dauki matakin ne bisa doka.

Dan-Ali ya kara da cewar, wadanda lamarin ya shafa sun hada da wadanda aka same su da aikata laifuka ko kuma wadanda keda hannu a almundahana da kudaden gwamnati ko kuma laifukan da suka shafi rashawa.

A cewarsa, idan aikin garambawul din ya kammala, za a rage dogaro kan sojojin kasar cikin ayyukan da 'yan sandan kasar ne suka dace su gudanar da shi.

Ya ce, ma'aikatar tsaron kasar na gudanar da aiki tare da ma'aikatar harkokin cikin gida, domin tabbatar da ganin an tantance ayyukan da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro suka dace su gudanar domin samar da kyakkyawan tsaro a kasar. (Ahmed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China